Daga Hassan Umar Gwammaja
Gwamnati Jihar Kaduna ta rushe wata Makaranta da Asibiti mallakar wasu ‘yan Kungiyar Shi’a Magoya Bayan Sheikh Ibarahim Zakzaky a Unguwar Rigasa Dake Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna
A cewar shugaban kungiyar ‘yan Shi’a reshen jihar Kaduna Aliyu Umar wanda ake yiwa lakabi da Tirmizi yace muna da damar mallakar duk abin da muke so a karkashin dokokin Najireya,
Sannan ya kuma kara da cewa mu a matsayin muna ‘yan uwa Musulmi almajiran Malam Zakazaky mun yi Allah wadarai da faruwar wannan abu da gwamnatin ta yi, har a zo a rusa gurarin da al’umma suke amfana.