An yi kira ga mawadata da kuma masu hannu da shuni su riga taimakawa marayun dake fadin kasar nan
Kiran ya fitone daga bakin Mai Unguwar Sabon Garin Unguwar Ma’azu dake Karamar Hukumar Kaduna Ta Kudu a cikin garin Kaduna Alhaji Sani Danmaje a yayin mikawa wasu marayu mukullin gidajen da Kungiyar Rabitul Almil Islami, Kungiyar Taimako Ta Duniya dake a kasar Sau’diya (Musulm World League) Taimakawa wasu marayu ta gina masu gidajen a unguwanin; Hayin Malam Bello da Nariyya da kuma Sabowar Unguwar Ma’azu a Kaduna
Dayake jawabi a gurin bada mukullayen Babban Daraktar kungiyar a nan Najireya Imam Al’amin Ahmad Hamza ya bayyana cewar wannan tallafine da yake zuwa daga wasu shehunan malamai kuma mawadata dake a kasar Sau’diya wanda suke bada tallafin kudadin a taimakawa marayun da haifinsu ya rasu yabar mata da ‘ya’ya basu da mahalli sannan ga filin ya bar amma babu yarda za su gina, sai kungiyar ta ji tagani saita ginamusu.
Malama Hajara Zubairu ita ce Uwar Marayu da aka ginawa gida a Sabowar Unguwar Ma’azu tace kimanin shekarau 5 ke nan da rasuwar mai gidanta ya bar mata ‘ya’ya 4 biyu maza biyu mata a duniya ta bayyana farcikinta da kuma jidadin ga wannan Kungiyar ta kasar Sa’udiya.