Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi bakuncin shugaban kamfanin Ɗangote Group, Alhaji Aƙiko Ɗangote, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa Ɗangote ya kaucewa zantawa da manema labarai na gidan gwamnatin tarayyar bisa hujjar cewa zai sake dawowa Villa a mako mai zuwa
A rahoton Punch, Ɗangote ya ce a mako mai zuwa zai sake ziyartar shugaba Tinubu tare da fitaccen Attajirin nan na duniya kuma shugaban kamfanin Bill and Melinda Gates Foundation, Bill Gates.