Yadda asusun bada tallafi na kasar China ya tallafawa sama da mutane 250,000 a kasar Habasha

Asusun raya kasashe masu tasowa na kasar China wato CFRD a takaice, ya samu yabo da jinjina, bisa managartar ayyukansa da ya gudanar a kasar Habasha, a dai dai lokacin da aka yi bikin cikarsa shekaru 3 da bude ofishinsa a kasar ta Habasha.

Asusun CFRD ya fara gudanar da ayyuka daban daban a Habasha tun daga shekarar 2015, an kuma yi masa rajistar gudanar da ayyuka a matsayin asusun ba da tallafin jin kai na kasa da kasa a kasar a watan Yulin shekarar 2019, inda ya maida hankali ga zurfafa hadin gwiwar musaya tsakanin al’umomin kasar Sin da na kasar Habasha.

Da yake jawabi yayin bikin na bana, babban daraktan kungiyoyi masu zaman kansu na kasar Habasha Jima Dilbo, ya ce asusun CFRD ya shafe shekaru 7 yana gudanar da ayyuka daban daban a Habasha, ciki har da ciyar da daliban makarantu, da raba kayan karatu, da kayan abinci, da ruwan sha da ayyukan tsaftar muhalli, da ayyukan bunkasa tattalin arzikin mata, ayyukan da suka amfani sama da ’yan kasar Habashan 250,000.

Mr. Dilbo ya kara da cewa, dukkanin ayyukan CFRD, sun yi daidai da muhimman ayyukan da gwamnati da al’ummun Habasha ke bukata, wadanda ke da matukar tasiri ga ci gaban kasar. Jami’in ya kuma yi kira ga asusun na CFRD, da ya jagoranci kungiyoyi masu zaman kansu dake Habasha, wajen kulla alaka da sauran kungiyoyi da hukumomi na kasa da kasa, kamar shirin samar da ci gaba na kasa da kasa, da na hadin gwiwar bunkasa kasashe masu tasowa, da shirin ziri daya da hanya daya.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments