Yadda taurarin Dan Adam suka fara zama barazana ga samun daddadan yanayi a sararin samaniya

Idan muka kalli sama, taurarin dan adam muke gani maimakon taurari.

Duk da yake taurarin dan adam da ke nesa ba matsala ba ne, taurarin dan adam da ke kusa da duniya da aka harba don aiyuka irin su yanar gizo suna zama matsala ga binciken kimiyya da nazarin taurari.

Daya daga cikin matsalolin da ke tasowa yayin da yawan jama’a ke karuwa kuma biranen duniya ke bunkasa, shine gurbataccen haske. Yanzu hasken sararin sama ya karu tare da gurbataccen haske. Sakamakon haka, mutane, musamman wadanda ke zaune a manyan birane, ba sa iya ganin abubuwan sararin sama da idannu da daddare, sai dai taurari masu haske sosai, rukunin taurari, duniyoyin da ke kusa ko wata.

Da kasancewar wannan al’amarin, ba abun mamaki bane ba a iya ganin damin taurari na “Milky Way” a cikin manyan birane. Musamman tare da habaka a fasahar tauraron dan adam da kamfanoni masu zaman kansu da kuma cibiyoyin gwamnati ke yi, wata sabuwar matsala ta yawan taurarin dan adam fiye da kima ta bullo.

Daga Sputnik 1 zuwa yanzu

Yawan taurarin dan adam da aka aika daga duniya zuwa sararin samaniya a yau ya zarce dubu 11 kuma adadin taurarin dan adam da ke yawo a sararin samaniya ya zarce dubu 7.

Yawan wadanda ke aiki daga taurarin dan adam din ya kai 4 dubu. Wasu kuma na jira a harba su ko kuwa an sanya su a matsayin tarkacen sararin samaniya.

Tun lokacin da Tarayyar Soviet ta harba tauraron dan adam, Sputnik 1 na farko a shekarar 1957, an aika dubban taurarin dan adam zuwa sararin samaniya don binciken kimiyya, yanayin sararin samaniya, sadarwa da dalilai na soji. A halin yanzu, Amurka tana da taurarin dan adam dubu 2 da 27, China na da 224, Birtaniya na da 129, Rasha na da 83 kuma Japan tana da 82.

Aikin sanya ido kan duwatsun “asteroid” da daukar hotuna

Bangarori biyu da taurarin dan adam suka fi shafa su ne Aikin sanya ido kan duwatsun “asteroid” da kuma daukar hotunan sararin sama. Musamman mutanen da ke sha’awar kallon sararin sama suna fuskantar matsaloli tare da taurarin dan adam da ke kusa da duniya. Don guje wa matsaloli, akwai manhajoji, shafukan yanar gizo da manahajojin wayar hannu wadanda ke nuna lokutan da taurarin dan adam ke wucewa.

Duk da haka, har yanzu ba a iya shawo kan matsalar ba, saboda yawan taurarin dan adam na karuwa da sauri. Aikin ‘Starlink’ na Elon Musk yana da nufin sanya dubban taurarin dan adam a duniya don aikace-aikacen yanar gizo wandanda zasu isa duk fadin duniya.

Hakanan yana shafar idanuwa

Taurarin dan adam da ke kusa da duniya na kuma shafar binciken kimiyya. A ko da yaushe ana sa ido kan sararin sama da muhimman na’urorin hangen nesa kamar na’urar hangen nesa mai tsayin mita 4 da Türkiye ke ginawa a Erzurum. Wasu daga cikin wadannan binciken na mai da hankali kan duwatsun “asteroid”. Ana bincike kan kananan duwatsun “asteroid” da ke kusa da duniya a wurare daban-daban, musamman ma kafin fitowar rana, ana kuma kididdige hanyoyin da suke bi.

Ana dubawa ko dutsen “asteroid” zai wuce ko kuma zai yi karo da duniya. Taurarin dan adam da ke kusa da duniya na da mummunan tasiri ga wadannan aiyukan sanya ido. Hukumar Bincike kan Sararin Samaniya ta Amurka (NASA) ta kafa Ofishin Kula da Tsaro na Sararin Samaniya (PDCO) don wannan dalilin.

Ana ci gaba da neman hanyoyin magance wadannan matsalolin da suka kunno kai a duniya baki daya.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments