Rahotanni na nuni da cewa kasar Turkiyya ta samu tagomashi mai yawa a wannan karo ta yadda tattalin arzikin ta ya daga izuwa sama.
Ministan Kudi da Baitulmali, na kasar Nureddin Nebati, shine ya bayyana hakan ga manema labarai a wani jawabi da ya gabatar.
Nebati ya ce, “Muna ci gaba da banbance tattalin arzikinmu daga na duniya ta hanya mai kyau, sakamakon babban ci gaba da karuwar aikin yi da muka samu.”
Nabati ya kara da cewa a yanzu haka adadin marasa aikin yi a kasar ta Türkiye ya ragu sosai da kaso mai yawa.