Shinkafa
Zogale
Mai
Tattasai
Albasa
Nama ko kifi
Maggi
Gishiri
Yadda ake Hadawa
Ki bada a barzo shinkafa saiki sa rariya tankaden gari ki fidda gari Dan kar dambun ya hade. Saiki wanke shinkafar da aka barza ki yanka nama kanana cikin ta saiki zuja su hade ki zuba ga abunyin dambu, Saiki yanka tarugu albasa da tattasai ki hada da zogale ki wanke. Saiki kwashe danbun da kika Dora a wuri mai fadi ki zuba su zogale da maggi da gishiri kiyayyafa ruwa ki juya suhade ki mayar ya qara turara idan yayi ki sauke kiss mai shikenan. Amma idan da steamer zakiyi komai zaki zuba a shinkafar ki zuba. Amma idan da abun yi na gargajiya zakiyi yafi kyau ayi bugu 2 yadda nayi bayani. Kuma idan kinaso zaki iya sa su karas,nidai da kifi nayi amfani aci lafiya.