Kasancewar bikin Salla lamari ne da ake da bukatar al’ummar Musulmai su nuna farin cikin su da walwala ta hanyar godewa mahaliccin su tare da yabawa jagoran halittu Annabi Muhammad S. A. W.
Hakan ce ta mabiya Darikar sheikh abdulkadir jiyani wadda aka fi Sani da kadiriya suka gudanar da taron zikirin hallara na tsawon yini guda a Unguwar Gwammaja layin Audu mai kusa.
Taron zikirin ya gudana ne a Unguwar Gwammaja kofar gidan Alh. Audu mai Kusa karkashin jagorancin Mal Ibrahim Musa Mai Kusa.
Zikirin ya gudana daki-daki inda Mukaddami Malam Muhammad Salisu Umar Gabari ya ja daga karfe biyu zuwa hudu.
A nasa bangaren jagoran zikirin ya fadi dalilan da yasa suka hada wannan daira ta hallar inda yace yin hakan abune mai kyau musamm a irin wadannan kwanakin idi
Taron zikirin ya sami halartar manya shehunnai na Darikar kadiriya na ciki da wajen jihar Kano.