Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada Hon. Alhassan Ado Doguwa ya bayyana bukatarsa ta tsayawa neman takarar shugaban majalisar wakilai ta goma da za’a kafa.
” Ina neman hadin kanku don ku sahalle min na zama Shugaban majalisar wakilai ta 10 don ciyar da kasar nan gaba, da kuma inganta aiyukan majalisa da kuma samar da cigaban ta kowacce fuska a Nigeria”.
Kadaura24 ta rawaito cikin wata wasika da Alhassan Ado Doguwa ya aikewa abokanan aikin sa yan majalisar, ya nemi hadin kan yan majalisar don zama Shugaban su.
” Ina taya ku murnar lashe zabukan ku wanda hakan ya baku damar kasancewa wannan majalisar, Ina so ku ajiye banbancin addini, kabilanci, bangaranci da kuma jam’iyyar siyasa ku bani dama don na zama Shugaban majalisa ta goma don cigaban Nigeria”. Inji Doguwa
Yanzu haka dai hankalin al’ummar Nigeria musamman ‘yan siyasa ya koma kan ganin waye zai zama Shugaban majalisa wakilai da kuma majalisar dattawa ta kasa.
Yan majalisu da dama dai sun fito don neman wadannan mukamai, sai dai zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu da jam’iyyar APC na kokarin ganin an sami shugabannin ba tare da yan shiga zabe ba.