Daga Hassan Umar Gwammaja
An yi kira ga mahukunta da kuma masu hannu da shuni suci gaba da taimawa masu bukata ta musamman domin hakan zai hanasu bara a kan tituna da sauran gurare.
Kiran ya fitone daga bakin mai girma sarkin makafin Bichi Alhaji Ibrahim Muhammed Dikko a zantawar sa da wakilin Aksam Media a fadarsa dake garin Bichi
Sarkin yayi kalamai masu nuni da bukatar mayar da hankali a kan masu rauni a cikin al’umma