Yadda masana suka gano hakorin Dan Adam mai shekara kimanin miliyan biyu a kasar Jojiya

Wasu masana Ilimin Kimiyyar Kayan Tarihi sun gano wani hakorin dan Adam a Jojiya da ke kasar Amurka, da ya kai shekaru miliyan 1.8.

Daga Walid Hari.

Wannan binciken nasu ya tabbatar na mutane farko-farko ne da suka yi rayuwa a nahiyar Turai.

An gano hakorin a kusa da kauyen Orozmani mai tazarar kilomita 100 daga Kudu maso Yammacin Tbilisi, babban birnin Jojiya da kuma kusa da Dmanisi.

A garin na Dmanisi ne a karshen shekarar 1990 zuwa farkon 2000, aka gano kokon kawunan mutane wadanda aka yi hasashen sun kai shekaru miliyon 1.8. a karkashin kasa.

Binciken ya gano cewa, mutanen sun yi rayuwa a shekarun da suka shude bayan sun yi kaura daga nahiyar Afrika.

Shugaban masu binciken Giorgi Bidzinashbili ya ce, suna hasashen hakorin na daya daga kabilar Zezva ko Mzia ne, wadanda a baya aka gano kokon kawunansu, wanda ya nuna sun yi rayuwa a baya sama da shekaru miliyon 1.8 a yankin.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments