Labaran Kasuwar yan kwallo

Daga Walid Hari

Southampton ta yi shirin sallamar kocinta, Ralph Hasenhuttl sakamakon rashin taka rawar ganin tun farkon wannan kaka. (Telegraph – subscription required) .

Akwai yiwuwar kocin Nottingham Forest Steve Cooper ya maye gurbin Hasenhuttl a St Mary. (Mail).

Kocin New York Red Bulls Gerhard Struber shi ma na daga cikin mutanen da Forest ke lissafin yiwuwar dauka. (Sun).

Liverpool za ta duba yiwuwar dauko É—an wasan Bayern Munich mai shekara 19 asalin Jamus da ke buga tsakiya, Jamal Musiala a sabuwar kaka, idan suka gaza daidaitawa da É—an wasan Borussia Dortmund asalin Ingila Jude Bellingham. (Mirror).

Barcelona ta amince da sayar da Antonie Griezmann mai shekara 31 ga Atletico Madrid kan rabin kudi euro miliyan 40 da aka nema. Dan wasan asalin kasar Faransa yanzu haka na zaman aro a Atletico.(Marca – in Spanish).

Everton za ta biya £4.5m domin mayar da zaman aro da Conor Coady ɗan Ingila ke yi daga Wolves na dindindin kafin karshen kaka. (Telegraph).

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments