Amurka ta nuna damuwar ta a fili da yadda Rasha da China suka goyi bayan Koriya ta Arewa

Daga Walid Hari

Amurka ta caccaki Rasha da China inda take zarginsu da goyon bayan Koriya ta Arewa da kuma kare ta daga takunkuman Majalisar Dinkin Duniya kan shirye-shiryen Koriyar na makamai masu linzami.

A yayin wani taro na tsaro, jakadan Amurka ya zargi Moscow da Pyongyang da bai wa Koriya ta Arewa kariya mai ƙarfi ta hanyar watsi da duk wasu takunkumai da aka bijiro da su domin ƙaƙaba mata.

Sai dai wakilan China da Rasha sun ce yawan tattaunawa ya fi alheri fiye da hukunci.

Sai dai jim kaÉ—an bayan haka ne kuma aka ji Koriya ta Arewa ta sake harba wani makami mai linzami da ke cin gajeren zango a cikin tekun Japan.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments