Xi ya yi alwashin matsa kaimi wajen yakar da cin hanci da rashawa a kasar China

A jiya  Litinin 13 ga watan Maris shekara ta 2023, aka kammala taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar China ta NPC a  birnin Beijing, fadar mulkin kasar.

Shugaban kasar China, kana babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kwamitin kolin rundunar sojan kasar Sin Xi Jinping a cikin jawabinsa a yayin bikin rufe taron ya bayyana cewa, tilas ne a karfafa raya jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin.

Yace ko da yaushe tafiyar da harkokin jam’iyyar a tsanake ba tare da kasala ba shine babban abin da zai saka a gaba kuma zai kara kaimi wajen yin yaki da cin hanci da karbar rashawa ba kakkautawa

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments