CBN ya Umarci bankuna da su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun 1000, 500 da 200

Babban Bankin tarayya ya amince da umarnin kotu na ci gaba da amfani tsofaffin takardun 200, 500 da1000 har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2023.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan kula da harkokin hulda da jama’a na bankin, Dakta lsa AbdulMumin ya fitar, Inda ya ce an cimma wannan matsayar ne a wani taro na kwamitin bankunan.

“A bisa bin ka’idoji da biyayya ga kotu, CBN a matsayin mai kula da bankunan kasuwanci, ta umarce su da su cigaba da karɓar da Kuma bada tsofaffin kudin kasar kamar yadda kamar yadda hukuncin kotun koli ya zartar wanda aka yanke a ranar 3 ga Maris”.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments