Jam’iyyar APC ta sauya tsarin da zata yi amfani da shi a zaben fidda ɗan takarar gwamnan jihar Kogi
A wata wasiƙa da APC ta aike wa hukumar zaɓe INEC, jam’iyya mai mulki ta aminta da zaben kato bayan ƙato wajen fidda ɗan takara
A ranar Jummu’a 14 ga watan Fabrairu, APC ta shirya gudanar da zaɓen amma ta ce zata ƙirga kuri’u washe gari
A yanzu, jam’iyyar mu mai albarka APC ta sake nazari kan matakan da zata yi amfani da su a zaɓen fidda ɗan takarar gwamna a Kogi kuma ta amince ta koma tsarin kato bayan kato maimakon na Deleget da ta sanar a baya.”
“Dangane da takardarmu ta farko mai kwanan watan 25 ga watan Janairu, 2023, mai lamba APC/NHDQ/INEC/19/023/191, wanda muka sanar da hukumar INEC tsarin da zamu bi wajen fidda ɗan takarar gwamna a jihar Kogi.
“Ranar zaben fidda gwanin na nan kamar yadda muka tsara watau ranar Jummu’a 14 ga watan Afrilu, 2023. Don haka zamu shirya taro na musamman don tantance ɗan takarar da ya samu rinjayen kuri’u ranar 15 ga watan Afrilu.”