Kungiyar marubuta wasanni ta jihar kano,ta bayyana gamsuwarta da yadda gasar wasannin kwallon kafa da ake gudanarwa a nan jihar kano yake gudana.
Sakataren kwamatin gudanar da wasannin na kungiyar Abdulgaffar Oladimeji ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai Jim kadan bayan kammala mikawa wasu daga cikin kungiyoyin kwallon kafa dake cikin gasar Wanda ya gudana a filin wasanni na Sani Abacha dake nan kano.
Abdulgaffar Olajimedi ya bayyana cewa, Sarkin Yarbawa na jihar kano da kamfanin (BETWGB)suka dauki Nauyin gasar Wanda aka yiwa Lakabi da Samar da zaman Lafiya.
Yace, an Samar da gasar ne domin sada zumunta da zaman lafiya tsakanin alumomi da kabilu daban daban dake kasar nan, musamman ma nan jihar kano da kungiyoyin kwallon kafa dake kananan hukumomi na jihar nan.
Ya bayyana cewa, wannan sabuwar Gwamnati mai ci sai tayi aiki tukuru wajen bijiro da tsare tsare da za su taimaka wajen bunkasar harkokin wasanni na jihar kano, musamman kwallon kafa Wanda matasa ne suke yinta kodayaushe,inda yace, Sarkin Yarbawa da kamfanin sune suka dauki nauyin kyaututtukan da aka rabawa kungiyoyin kwallon kafar sakamakon jajircewa da kwazo da suke nunawa wasannin.
Ya kara da cewa,daga cikin kyautukan da aka rabawa kungiyoyin, akwai riguna da kalanda da sauran kayayyakin da suka shafi kwallon kafa, Inda ya bayyana cewa, kungiyoyi da dama sun samu wannan kyaututtukan,kamar kananan hukumomin Kibiya da Takai da Sumaila da Gwale da kuma, wasu kungiyoyin kwallon kafa na wasu daga cikin jihohin Najeriya, kamar jihar Kwara da dai sauransu.
A jawabinsa Sarkin Yarbawa Dr. Murtala Ahmi Otutesi,ya sha alwashin ci gaba da ba da Tallafi ga kungiyoyin kwallon kafar Domin Samar da hadin kai da zaman lafiya tsakanin Alumma, musamman matasa,inda yayi alkawarin daukar nauyin kyaututtukan da za,a baiwa wadanda suka samu Nasara a Gasar, Domin kara Samar da zumunta da zaman lafiya.
Dr.murtala ya kuma bayyana cewa, za su kara tattaunawa da Ibrahim Galadima a matsayinsa na Uba kuma, Masani a harkokin wasanni yadda za su hada hannu guri guda domin baiwa Shugabannin kungiyoyin kwallon kafa horo na musamman domin yin gogayya da sauran kungiyoyin wasan kwallon kafa na kasashen Duniya.
Yace, rashin baiwa Shugabannin kungiyoyin kwallon kafa horo na daya daga cikin abubuwan da suke mayar da kasar nan koma baya a fannin harkokin wasanni.
Haka zalika,Sarkin Yarbawa Dr Murtala Ahmi Otutesi,ya yabawa kungiyar marubuta wasanni da kwamatin shirya gasar, Musamman Abdulgaffar Oladimeji daya yi ta kai kawo wajen ganin komai ya tafi yadda ya kamata,inda yace,ya Dade yana ba da gudunmawa a harkokin wasanni yadda ya dace.
Daga karshe Sarkin ya jaddada kudirinsa na kawo sauye_sauye a fannin harkokin wasanni a kasar nan, musamman a jihar kano wadda ake alfahari da koyi da ita ta fannoni da dama,haka kuma,ya nuna mutukar farin cikinsa bisa yadda kungiyoyin kwallon kafan suka ba da hadin kai ba tare da wata Rigima ba.
Ibrahim sani gama pyramid radio.