Lauya mai rajin gwagwarmaya da kare hakkin Dan Adam a jihar Kano Barr. Badamasi Suleiman Gandu, ya gabatar da takardar korafi ga kwamishinan yan sandan jihar Kano inda ya bukaci rundunar yan sandan jihar ta binciki masu daukar bidiyon wani A. A. Rufa’I wanda yake ikirarin yafi kowa kudi a duniya.
Barr. Gandu ya rubuta korafin nasa mai shafi uku inda ya gabatar da shi ga kwamishinan yan sanda CP Usaini Gumel.
A sakon da Barr Gandu ya aikowa jaridar Aksammedia yace sun ga dacewar shigar da korafin ne domin bada Kariya ga A A Rufa’i wanda ke fama da rashin lafiyar kwakwalwa.
Ko makon da ya gabata ahlin A A Rufa’i a zantawar su da Dala Fm sunce a shirye suke domin daukar matakin shari’a ga masu tunzura Dan uwan nasu ta hanyar bashi kwaya a cikin lemo yana sha yana kara yin jawabin na rashin nutsuwa.
A aciki irin jawabin nasa A A Rufa’i yace tuni ya sayi wasu kashe na duniya da kulab kulab na kwallon kafa kuma ya biya.