• About Us
  • Advertisiment
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
  • Radio
AKSAM MEDIA
No Result
View All Result
No Result
View All Result
AKSAM MEDIA
No Result
View All Result
Home HAUSA NEWS

Wasu Karin cutuka da ake dauka daga Dabbobi zasu Iya barkewar a Africa: WHO

Aksam Media by Aksam Media
October 8, 2022
in HAUSA NEWS
0
0
SHARES
Share on FacebookShare on Twitter

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana hasashen ta na cewa, nahiyar Afirka na fuskantar barazanar barkewar wasu kwayoyin cututtuka da ake dauka daga namun daji zuwa ga mutane, kamar irin kwayar cutar kyandar biri, wadda ta samo asali daga dabbobi. sannan ta sauya kama inda ta kama mutane.

A rahoton da ta fitar WHO ta ce, an samu karuwar kashi 63 cikin 100 na barkewar kwayoyin cuta dake yaduwa daga dabbobi zuwa mutane a yankin na Africa daga shekarar 2012 zuwa 2022, idan aka kwatanta da makamancin lokacin daga shekarar 2001 zuwa 2011.

RelatedPosts

Masarautar Kano ta daga darajar wasu Hakimai tare da nada wasu sababbi

Masarautar Kano ta daga darajar wasu Hakimai tare da nada wasu sababbi

March 31, 2023
INEC ta mika shahadar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar Kaduna

INEC ta mika shahadar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar Kaduna

March 31, 2023

Russia ta kama wani Dan Amurka mai leken asiri

March 30, 2023

A cewar wata sanarwar da ofishin WHO na
yankin Afirka ya fitar ya bayanin cewa, wani sabon bincike da hukumar ta gudanar ya ba da rahoton al’amuran kiwon lafiyar jama’a 1,843 da aka tabbatar a yankin Afirka, tun daga shekara ta 2001, kuma kashi 30 cikin 100 na wannan matsala, suna da nasaba da barkewar cututtukan da ake dauka daga namun dai, kamar su cutar Ebola, da zazzabin Dengue, da Anthrax, da annobar Plague, da cutar kyandar biri da sauran ire-iren su.

Bisa la’akari da karuwar bullar cutar kyandar biri a baya-bayan nan, tun daga farkon bana, kasashe da yankuna 75 sun gabatar wa hukumar rahotanni kan yadda mutane fiye da dubu 16 suka kamu da cutar, ciki had da wasu 5 sun mutu, wadanda dukkansu suka fito daga kasashen Afirka.

Hukumar WHO ta yi gargadin cewa, karuwar yawan jama’a a nahiyar Afirka, tana haifar da bunkasar birane da kuma kutse ga muhallin namun daji, wanda ke kara hadarin barkewar cututtukan da jama’a ke dauka daga dabbobi, daga yankuna marasa ci gaba dake da karancin mazauna zuwa manyan birane.

Darektar WHO mai kula da ofishin yankin Afirka Matshidiso Moeti ta bayyana cewa, duk da ingancin harkar sufuri a Afirka, ana samun karuwar barazanar cututtukan da jama’a ke dauka daga dabbobi da ke kara shiga manyan birane. Don haka ta ce, tilas ne mu dauki mataki ba tare da bata lokaci ba, don magance wadannan cututtuka, kafin su yadu da hana Afirka zama wuri na kamuwa da cututtuka.

Dakile yaduwar irin wadannan cututtuka a Afirka yana da sarkakiya, kuma WHO ta ba da shawarar amfani da tsarin kiwon lafiya na bai daya, wanda ke bukatar sassa da dama, da fannonin ilmi, da al’ummomi domin yin aiki tare. Wannan ya kunshi masana, ciki har da wadanda ke aiki a fannin lafiyar bil-Adam, da dabbobi, da muhalli. Haka kuma ya kamata a raba bayanan sa ido na yau da kullum game da cututtuka da ayyukan mayar da martani, ga lafiyar dabbobi da na dan Adam a tsakanin masana cututtuka da sauran masana kiwon lafiyar jama’a.

Moeti ta ce, “Muna bukatar gudummawar kowa da kowa, don kandagarki da dakile yaduwar cututtukan dake yaduwa daga dabobbi zuwa ga mutane kamar Ebola, da cutar kyandar biri, da dai sauransu.” Tana mai cewa, bazuwar cututtuka daga namun daji zuwa mutane, tana faruwa daga abubuwan da suka faru daga dabbobi zuwa mutane. Don haka ta ce, sai mun kawo karshen matsalolin dake tsakanin wadannan bangarori, kafin mu iya magance duk wani bangare na matakin da za a dauka.

Tun daga shekara ta 2008, WHO ta inganta hadin gwiwa da hukumar abinci da aikin noma ta MDD, da hukumar kula da lafiyar dabbobi ta duniya, don taimakawa kokarin da ake yi na magance barkewar cututtuka daga dabbobi zuwa mutane a fadin Afirka.

A kwanakin nan, hukumomin uku sun yi aiki tare yayin da cutar Ebola ta barke a karo na 14, wadda aka ga bayan ta a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ba da dadewa ba.

ShareTweetSendSharePin
Previous Post

Daya daga cikin manyan guraren hakar danyen Mai na Kasar China ta samar da Ganga Biliyan 2.4 cikin shekara 60

Next Post

Kotu ta soke takarar wasu Yan Majalisa 12

Aksam Media

Aksam Media

RelatedPosts

Masarautar Kano ta daga darajar wasu Hakimai tare da nada wasu sababbi
HAUSA NEWS

Masarautar Kano ta daga darajar wasu Hakimai tare da nada wasu sababbi

by Aksam Media
March 31, 2023
0

Daga khadija Abdullahi Aliyu Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya daga Darajar wasu Hakimansa da kuma nada...

Read more
INEC ta mika shahadar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar Kaduna

INEC ta mika shahadar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar Kaduna

March 31, 2023
Russia ta kama wani Dan Amurka mai leken asiri

Russia ta kama wani Dan Amurka mai leken asiri

March 30, 2023
Hanya mai sauki da zaka hana sauro rayuwa a inda kake

Hanya mai sauki da zaka hana sauro rayuwa a inda kake

March 30, 2023
Makaman da ake Dari-dari kar Rasha tayi amfani da su akan Ukraine yanzu ta fara

Makaman da ake Dari-dari kar Rasha tayi amfani da su akan Ukraine yanzu ta fara

March 29, 2023
Rarara ya saki zazzafar Wakar da yayi wa Abba Gida-gida ta cin zabe

Rarara ya saki zazzafar Wakar da yayi wa Abba Gida-gida ta cin zabe

March 29, 2023
0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Login
Notify of
guest
guest
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments
  • Trending
  • Comments
  • Latest
Kamfanin MTN  ya canza hanyoyin saka Kati da siyan data da duba Balas

Kamfanin MTN ya canza hanyoyin saka Kati da siyan data da duba Balas

March 10, 2023
Rarara ya saki zazzafar Wakar da yayi wa Abba Gida-gida ta cin zabe

Rarara ya saki zazzafar Wakar da yayi wa Abba Gida-gida ta cin zabe

March 29, 2023
Yanzu-yanzu: INEC ta fitar da sabuwar Sanarwa

Yanzu-yanzu: INEC ta fitar da sabuwar Sanarwa

February 21, 2023
INEC tayi umarnin kara gudanar da zabe a jihar Kogi

Sakamakon zabe na kananan hukumomi 34 na jihar Kano

March 19, 2023
CBN za ta bayar da tallafi ga graduate ku shiga nan kuyi register

CBN za ta bayar da tallafi ga graduate ku shiga nan kuyi register

2
Latest News On N-Power Stipends For Today September 5th, 2022.

Latest News On N-Power Stipends For Today September 5th, 2022.

1
Masu tura finafinan Hausa sun koka da rashin samun tallafi daga gwamnati duda dinbin yawan da suke dashi

Masu tura finafinan Hausa sun koka da rashin samun tallafi daga gwamnati duda dinbin yawan da suke dashi

1
Kungiyar masu hada-hadar wayoyin hanu ta jihar Kano ta shirya gasar kwallon kafa ga yayanta dake fadin jihar Kano.

Kungiyar masu hada-hadar wayoyin hanu ta jihar Kano ta shirya gasar kwallon kafa ga yayanta dake fadin jihar Kano.

1
Masarautar Kano ta daga darajar wasu Hakimai tare da nada wasu sababbi

Masarautar Kano ta daga darajar wasu Hakimai tare da nada wasu sababbi

March 31, 2023
INEC ta mika shahadar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar Kaduna

INEC ta mika shahadar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar Kaduna

March 31, 2023
Russia ta kama wani Dan Amurka mai leken asiri

Russia ta kama wani Dan Amurka mai leken asiri

March 30, 2023
Hanya mai sauki da zaka hana sauro rayuwa a inda kake

Hanya mai sauki da zaka hana sauro rayuwa a inda kake

March 30, 2023
  • Kamfanin MTN  ya canza hanyoyin saka Kati da siyan data da duba Balas

    Kamfanin MTN ya canza hanyoyin saka Kati da siyan data da duba Balas

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Rarara ya saki zazzafar Wakar da yayi wa Abba Gida-gida ta cin zabe

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Yanzu-yanzu: INEC ta fitar da sabuwar Sanarwa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sakamakon zabe na kananan hukumomi 34 na jihar Kano

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Yadda wata makaranta mai dauke da tarin marayu suka yi bikin saukar Al-qur’ani

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Masarautar Kano ta daga darajar wasu Hakimai tare da nada wasu sababbi
HAUSA NEWS

Masarautar Kano ta daga darajar wasu Hakimai tare da nada wasu sababbi

Daga khadija Abdullahi Aliyu Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya daga Darajar wasu Hakimansa da kuma nada ...

March 31, 2023
INEC ta mika shahadar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar Kaduna
HAUSA NEWS

INEC ta mika shahadar lashe zabe ga zababben gwamnan jihar Kaduna

Hukumar Zabe Mai Zaman Katta Ta Kasa INEC, yau tabawa zabban Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Malam Uba Sani shedar sakamako yin ...

March 31, 2023
Russia ta kama wani Dan Amurka mai leken asiri
HAUSA NEWS

Russia ta kama wani Dan Amurka mai leken asiri

An kama wani ɗan jaridan Amurka da ke aiki da jaridar Wall Street Journal a Rasha inda aka zarge shi ...

March 30, 2023
Hanya mai sauki da zaka hana sauro rayuwa a inda kake
HAUSA NEWS

Hanya mai sauki da zaka hana sauro rayuwa a inda kake

A duk lokacin da kake da bukatar ko kike da bukatar korar Sauro akwai hanya mai sauki da zaku yi ...

March 30, 2023
Makaman da ake Dari-dari kar Rasha tayi amfani da su akan Ukraine yanzu ta fara
HAUSA NEWS

Makaman da ake Dari-dari kar Rasha tayi amfani da su akan Ukraine yanzu ta fara

Rundunar sojin Rasha ta yi amfani da tsarin Tornado-G wajen harba rokoki da dama a lokaci guda kan cibiyoyin sojan ...

March 29, 2023

Recent Comments

  • Ibrahim S kabara on Hukumar kula da ayyukan yan sanda ta raba lambobin kiran waya Dan sa Ido a ayyukan yan sanda a lokacin zabe
  • Abbas Jibril on Katu ta Yankewa AbdulJabbar Kabara Hukuncin Kisa ta hanyar Rataya
  • Walid Y Haris on Akwai Malaman cocin dake kallan batsa a yanar gizo ta wayoyinsu-Fafaroma
  • Abba Garba Sufi on Kungiyar masu hada-hadar wayoyin hanu ta jihar Kano ta shirya gasar kwallon kafa ga yayanta dake fadin jihar Kano.
  • Sani saadu aliyu on CBN za ta bayar da tallafi ga graduate ku shiga nan kuyi register
  • About Us
  • Advertisiment
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
  • Radio

© 2023 Aksam Meadia LLC

No Result
View All Result
  • About Us
  • Advertisiment
  • Contact Us
  • Home
  • Privacy Policy
  • Radio

© 2023 Aksam Meadia LLC

wpDiscuz