Babbar Kotun tarayya dake zama a Patakwal ta soke tikitin ‘yan takarar majalisar jihar Rivers 12 na jam’iyyun African Democratic Congress (ADC) da Action Democratic Party (ADP).
Jaridar Punch ta ruwaito cewa alƙalin Kotun, mai shari’a Turaki Mohammed, ya amince tare da abinda jam’iyyar PDP ta gabatar masa cewa jam’iyyun sun karya dokokin zaɓe 2022 yayin gudanar da zaben fidda gwaninsu.
Babbar Kotun tarayya dake zama a Patakwal ta haramta wa yan takara 12 na majalisar dokokin jihar Ribas shiga zaɓen 2023 ne sabo da korafin da babbar jam’iyar adawa ta PDP ta shigar
Hukuncin Kotun ya shafi yan takara 7 na jam’iyyar ADC da kuma guda 5 na jam’iyyar ADP
Da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Muhammed, yace hukumar zaɓe INEC ba ta da hurumin amincewa da ‘yan takarar majalisar jiha 7 na ADC saboda hujjojin da aka gabatar masa sun nuna cewa jam’iyyar ta yi wa doka karan tsaye.
Lauyan ADC, Benibo, yace tawagar lauyoyi zasu yi nazari kan hukuncin Kotun, sannan su ɗauki matakin ko zasu ɗaukaka ƙara ko zasu hakura.
“Ina tunanin Alkali ya gano cewa jam’iyya ba ta ayyana a fili kan kalar zaben fidda gwanin da zata yi ba, ‘yar tinƙe, na Deleget ko masalaha. Yan takara 5 sun tsira yayin da Bakwai kuma suka rasa tikitinsu.”