Ministan tsaron Ghana Dominic Nitiwul, ya shaida wa majalisar dokokin kasar cewa wasu ‘yan tada zaune tsaye sun yi kokarin tarwatsa wata gada da bama-bamai a yankin Bawku da ke kusa da kan iyakar kasar da Burkina Faso.
Garin Bawku na cike da manyan bindigogi irin wadanda ya kamata sojojin Ghana su rike, amma matasa farar hula ne suke rike da su,, kuma suna amfani da su kamar babu gobe. Idan ba mu dauki batun Bawku da muhimmanci ba, lamarin zai haifar da matsaloli a kasar, a cewarsa.
Ministan ya kara da cewa abin da ke faruwa a yau ba rikicin sarauta ba ne, babban laifi ne. Wadanda ke aikata hakan miyagun mutane ne. Amma, ana kara tsaurara matakan tsaro a yankin, domin an kara yawan sojoji daga 50 zuwa 400 kuma za a kara tura 500 a cikin wannan makon.
Garin Bawku dai ya fada cikin rikici tsawon shekaru da dama, tsakanin al’umomi biyu masu gaba da juna, lamarin da masana ke fargabar zai iya haifar da rashin zaman lafiya tare da bai wa masu tsaurin ra’ayin addini damar kutsawa cikin Ghana. Sau da yawa ana samun tashe-tashen hankula tsakanin kabilun Kusasi da Mamprusi kan zabar sabon sarki a Bawku.
Adib Sani, masani ne kan tsaro, yace abin da ya sha fadi cewa masu tsattsauran ra’ayin addini za su iya amfani da rikicin sarauta da ke faruwa a Bawku su shigo Ghana zai iya tabbata, domin kokarin karya gada da abin fashewa abu ne da sojoji kawai ke iya yi ba masu ta da zaune tsaye ba
Halin da garin yake yanzu, a cewar dan majalisar gundumar Bawku Namanga Mushiri, wanda aka fi sani da Assembly-man ya bayyana, abin da ke faruwa a garin ya shafi gudanar da ibada, ilmin yara da kuma rayuwa baki daya. Ya kuma ce, suna bukatar addu’o’i daga al’umma domin a yanzu “kana tare da mutum an jima sai ka ji an kashe shi,” saboda rashin tsaro.
Kungiyar limaman cocin Katolika ta kasa, a wani taron manema labarai, ta yi kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki kan rikicin na Bawku, da su gaggauta kawo zaman lafiya a garin.