Ranar 13 ga watan Fabrairu rana ce da hukumar raya al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya da ake kira UNESCO ta ware a matsayin ranar rediyo ta duniya don hada kan al’uma a fadin duniya.
Rediyo kafa ce ta ilimantarwa, fadakarwa da kuma Nishadantarwa wadda kuma ke assasa kawo sauye-sauyen manufofi a kasa ta hanyar rahotannin da ake yadawa.
Taken ranar na wannan shekarar shi ne “Rediyio da Zaman Lafiya,” don jaddada wa al’ummomi rawar da redio ke takawa wajen samar da zaman lafiya.
Saboda muhimmancin ranar rediyo ta duniya, kungiyar masu sauraren rediyo da ake kira Radio Listeners Association a jihar Borno, ta karrama wasu gidajen rediyo na gida da waje, ciki har da Muryar Amurka (VOA).
Shugaban kungiyar Alhaji Abdulahi Dungus, ya ce sun karrama gidajen rediyon ne saboda irin gudummuwar da suke bada wa wajen yada labarai ba dare ba rana ta fannin tsaro, lafiya, zamantakewa, da sauransu.
Ya kara da cewa shirye-shirye na musamman da Muryar Amurka ke yi da kuma yadda gidan rediyon ke ba talaka damar ba da gudummowarsa, abin a yaba ne.
Idris Nuhu Waziri, mai ba kungiyar Radio Listeners Association shawara ta fuskoki da dama, ya ce rabin ilimin da suke da shi sun same shi ne ta rediyo, saboda wanda ke Najeriya ya san abubuwa, wurare da shahararrun mutane da yawa ta rediyo.