INEC ta ware wasu mazabu 240 da ba za’a gudanar da zabe ba
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa ba zata sami damar gudanar da zabe ba a wasu akwatina 240
Hukumar ta bayyana hakan ne ta bakin shugaban ta Farfesa Muhammad Yakubu a wani taron ganawa da juna da hukumar tayi da shugabanin jam’iyun siyasa