Ƴan bindiga sun kai farmaki kan tawagar motocin kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar Abia a birnin Aba
Ƴan bindigar sun farmaki kwambar motocin kwamishinan ne lokacin da yake tsaka da rangadin aiki a cikin birnin
Jami’an ƴan sanda biyu sun rasa rayukansu a mummunan harin, sannan ƴan bindigar sun kuma cinnawa ɗaya daga cikin motocin wuta