Gwamnatin jihar Bauchi ta tabbatar da rasuwar ɗalibai biyu a ƙaramar hukumar Jama’are a jihar a dalilin zargin ɓarkewar cutar Mashaƙo.!
Shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko na jihar Bauchi (BSPHCDA), Dr Rilwanu Mohammed, shi ne ya tabbatar da hakan yayin ganawa da manema labarai.
Jaridar Leadership ta tabbatar da cewa Cutar ta halaka dalibai guda biyu
Dr Rilwanu ya bayyana cewa daga cikin ɗalibai 58 da aka ɗauka, biyu daga ciki sun rasu a sakamakon cutar mashaƙon, yayin da ake ci gaba da gudanar da gwaji akan sauran.
Ya bayyana cewa hukumar sa a shirya take domin ganin ta hana yaɗuwar cutar, inda ya ƙara da cewa za a yi allura domin hana yaɗuwar cutar.
Dr. Mohammed ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta bayar da umarnin kulle dukkanin makarantun da abun ya shafa a ƙaramar hukumar domin yin takatsantsan da yaɗuwar cutar