Daga khadija Salisu Danmaliki
Ƙungiyar kwadugo ta ƙasa (NLC) ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 7 ta sake nazari kan tsare-tsarenta da suka haddasa tsadar rayuwa a Najeriya.
Jaridar Vanguard ta bayyana cewa NLC ta buƙaci gwamnatin tarayya ta janye waɗan nan tsare-tsare da suka jefa talakawa cikin halin ƙaƙanikayi, ciki harda tashin farashin litar man fetur na kwanan nan.
Ƙungiyar ta bada waadin mako guda ga gwamnatin tarayya ta sauya waɗannan tsare-tsaren na yaƙi da talakawa ko kuma a fuskancin yajin aikin gama gari daga ranar 2 ga watan Agusta, 2023