Matashin mai suna Dauda Ibrahim Abba ya hadu da ajalin sane yayin da suke tsaka da tafiya akan babur din su a kan titin Ring road by pass inda Motar Jamian na civil defense suka Kade su a rashin Sani
Bayan faruwar Lamarin basuyi wata-wata ba suka garzaya da su asibiti inda anan ne dauda yace ga garin ku nan
Lamarin ya faru ne a Daren Jiya kuma a safiyar yau Asabar aka yi masa janaiza kamar yadda addinin musulunci ya tanada shi kuma abokin marigayin yana gadon Asibiti yana cigaba da karbar magani.
Wakilin AKSAM MEDIA ABDULHAMID ISAH D Z ya zanta da iyayen marigayin Bayan kammala janaizar Dan nasu inda sukace
jamian Hukumar basu halarci wurin janaizar ba duda abin da sukayi na aron hanu a tuki ganganci ne, Mu ba zamu Iya ja da gwamnati Ba amma muna bukatar adalci