Hukumar ta kama Aremu Timothy Adeyboyegu dauke da miliyan 80 na CFA yayin da yake kokarin tsallake iyakar Ghana da Togo, a kan wani babur da ake tsallake iyakar da shi ta barauniyar hanya.
A zantawar sa da manema labarai, Babban kwamishinan hukumar kwastam ta kasar Ghana, Alhaji Saidu Idris Iddisa ya ce “mun kama shi da miliyan 80 na CFA, amma na jabu yayin da yake kokarin tsallake iyakar Ghana da Togo a Aflao akan wani babur. Yana dauke da fasfo din tarayyar Najeriya, a don haka zamu iya cewa shi dan Nijeriya ne duk da haka dai sai in mun tuntubi hukumomi a Najeriya. Ya fada mana cewa sako aka bashi ya bai wa wani a don haka muna bincike.”
Da yake tsokaci a kan lamarin, mai sharhi akan alamurran yau da kullum, Shariff Abdul Salam ya jinjinawa hukumar kwastam bisa wannan nasara da tayi wajen cafke mutumin kuma shigo da kudaden jabu a Ghana na baranza ga tattalin arzikin kasar saboda farashin kayayyaki ya tashi.
Hukumomi a kasar sun bayyana cewa za su ci gaba da kare iyakokin kasar na hana masu tsallake ta ba bisa kaida ba.
An bayaninsa, mai magana da yawun hukumar shige da fice a yankin WA ta kasar, Ibn Yusuf Durana, ya ce idan zaka shiga da kudi da yawa to ya kamata ka bayyana wa hukumomi saboda idan matsala ta zo za su iya warware ta. Ya kuma ja hankalin mutane da cewa idan suna rike da kudi da yawa ya kamata su rinka zuwa wajen hukumar shige da fice, domin karbar fom suna cikewa ko za su fita ko za su shiga, domin kauce karya doka.
Hukumar kwastam da ‘yan sanda sun sanar da fara gudanar da bincike mai kwarin gaske bisa wannan al’amari domin ajiye doka a mazauninta.