Daga Sadik Lamin Hassan
Majalisar Masarautar Katsina ta sanar da sallamar Makaman Katsina Hakimin Bakori Alhaji Idris Sule Idris daga mukaminsa.
Bayanin hakan na cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan wata 19 ga watan Janairun, 2023 mai dauke da sa hannun Kauran Katsina Alhaji Aminu Nuhu Abdulkadir.
Sanarwar ta ce bisa korafe-korafen da gwamnatin jihar Katsina ta samu game da Makaman Katsina, Hakimin Bakori, wanda ta sa Masarautar Katsina ta bincika kuma aka tabbatar da wadannan korafe-korafe.
Don haka, gwamnatin jihar Katsina tare da Masarautar Katsina sun tabbatar da sallamar Makaman Katsina Hakimin Bakori daga ranar Alhamis din nan 19, ga watan Janairun, 2023.
Aksam Media ta ba da labarin cewa a watan Nuwambar 2022 dai ne Masarautar Katsina ta sanar da dakatar da Hakimin har sai an kammala bincike a kan korafe-korafen da aka yi kansa.