Gwamnatin jihar Edo ta bada umurnin kama wasu Sarakunan gargajiya biyu tare da wasu mutum biyar da ake zargi da hannu a harin ta’addanci da aka kaiwa jirgin kasa a jihar a ranar 7 ga watan Janairu na 2023.,
A zantawar sa da manema labarai Kwamishinan Sadarwa na jihar, Chris Nehikhare, ya ce gwamnatin jihar Edo ta bada sanarwar kama wasu mutane biyar tare da wasu Sarakunan Gargajiya biyu da ake zargi da hannun kan harin jirgin kasa da ya yi sanadin sace akalla mutane 20 tare da jikkata wasu da dama.
Ya ce zuwa yanzu dai jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike kuma za’a gurfanar da su a gaban kuliya.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Edo, Chidi Nwabuzor, ya ce dukan wadanda aka ceto babu abin da ya same su kuma suna ci gaba da gudanar da bincike domin bankado abinda ya faru.
Wannan dai ba shi ne karon farko da aka kai hari da garkuwa da fasinjojin jirgin kasa a Najeriya ba, inda ko a shekarar da ta gabata an c yi garkuwa da wasu fasinjojin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna inda daga bisani ‘yan ta’addan su ka rika sako su rukuni-rukuni da bayanai ke nuni da cewa an biya kudin fansa.