Wani Dan damfara ya shiga hannun jami’an KAROTA bayan ya damfari wata mata 600,000

Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta sami nasarar cafke wani magidanci dan damfara bayan ya damfari wata kuɗi naira dubu ɗari shida (N600.000)

Jami’in hulda da jama’a na Hukumar Nabulusi Abubakar kofar Na’isa shine ya bayyana hakan ga manema labarai Inda yace Jami’an Hukumar KAROTA sun sami nasarar cafke magidancin mai suna John Bandes a kan titin Oba Sanjo Dake cikin birnin Kano.

A makon da ya gabata ne wata budurwa mai suna Jenifer Paul ta shigar da ƙorafi a Hukumar KAROTA bayan Damfarar da magidancin ya yi mata ta hanyar amfani da Baburin Adaidaita Sahu

Ta bayyana wa KAROTA cewa lokacin da ta hau Adaidaita Sahun watanni biyu da suka gabata, magidancin ya damfareta zunzurutun kudi har naira dubu ɗari shida.

An samu nasarar cafke Adaidaita Sahun mai lambar RRN 231QA da kuma Koriyar lambar FGE 19-0849

Magidancin mai suna John Bandes ɗan kimanin shekaru 45 ya bayyana wa Humar KAROTA ba shi kadai yake aikata Damfarar ba suna da yawa, kuma sun shafe fiye da wata shida suna Damfarar jama’a a nan Kano da babban birnin tarayyar Abuja

A binciken da Hukumar KAROTA ta gudanar ta gano yadda John ɗin ke amfani da wani sinadari a cikin wata kwalba, da zarar sun zubawa fasinja zai sami juyewar Kai, sai yadda suka yi da shi kamar yadda Janifer ta bayyana

Haka kuma Hukumar ta gano John ɗin ya jima yana aikata saƙa a mugun zare kafin dubunsu ta cika

Wani binciken sirri da KAROTA ta samu ya bayyana cewa fiye da watanni shida da suka gabata Rundunar ‘Yansanda ta baza koma wajen ganin an damke John ɗin sai a wannan rana dubunsu ta cika.

Tune dai Hukumar ta miƙa John ga ofishin Baturen ‘yansanda na Badawa domin faɗaɗa bincike tare da ɗaukar mataki na gaba

A ƙarshe Hukumar KAROTA na jan hankalin jama’a da su cigaba da sa ido a kan duk wani matukin Adaidaita Sahu kafin su hau domin gujewa faɗawa hannun ɓata-gari

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments