Daga Jamila Sulaiman Aliyu
Hukumar hisbah ta jihar Kano taja hankalin dakarunta dasu zage damtse wajen kyautata mu,amalalarsu da al’umma kasancewar shi Addini nasiba ne.
Kwamandan hukumar sheik Haroon muhd sani ibn sina shine yayi wannan kiran bayan dawowarsa daga kasa Mai tsarki inda gudanar da aikin ummara.
Ibn Sina yace baya ga ibada da mahalicci ya kallafa wa halittarsa wadanda suka kunshi tauhidi da sallah,Azumi,da zakka da hajji ba wani abu da ya Kai ma,amala don haka yake jan hankalin al’umma dasu kyautata mu’a malarsu a dukkan fannonin rayuwa.
Sheik Haroon muhd sani ibn sina yace da za,a kulaa da mu’amala a abubuwan da suka shafi zamantakewa da kasuwanci , auratayya hatta a abinhawa na haya, da kuma a mabambantan addinai da kowa ya zauna lfy a wannan rayuwar mai cike da kalu bale
.Babban kwamandan hukumar ya gargadi dakarun hukumar hisbah da suyi dukkan mai yiwuwa domin nusar da al’umma mahimmanci mu’amala mai kyau ga makwafta duba da yadda suke cin karo da matsalolin makwafta a hukumar da kuma tarin korafe korafe