Kifaye masu girman wuce kimanin na cigaba da mutuwa a kasar New Zealand

Rahotanni sun bayyana cewa wasu manyan kifaye nau’in “pilot whale” 240 da suka makale a tsibirin Pitt na kasar New Zealand, sun mutu.

Hukumomin kasar New Zealand sun bayyana cewa tawagar kwararru sun tantance yanayin kifayen 240 da suka makale, sannan aka kashe kifayen da suka tsira.

Dave Lundquis, Jami’in Ma’aikatar Kula da Kare Dabbobi da yake magana akan kashe kifayen ya ce, “Ba a taba daukar irin wannan shawarar ba tare da nazari ba, amma a cikin wannan yanayi shine zabi mafi kyau.”

Y a kuma bayyana cewa ba su yi kokarin mayar da wadanda suka tsira daga kifayen da suka makale cikin teku ba saboda hatsarin kifayen Mari, kana ya yi nuni da cewa, babu isassun kwararru a yankin da za su taimaka da wannan aikin.

A ranar 8 ga watan Oktoba, ne kifayen “pilot whale” 215 suka mutu a tsibirin Chatham, wanda ya ke kusa da tsibirin Pitt na New Zealand.

Har kawo yanzu a san dalilin da ya sa kifayen ke fitowa bakin tekun ba.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments