Shaljwatar tsaro ta kasa ta bayyana adadin yan taaddar da suka Mika wuya da adadin su yakai mutum 1755 bayan a rangamar da suka yi da jamian tsaro a jihar borno.
A ce war rahoton da shugaban sashin Yada labarai Manjo Jabar Benard Onyeuko ya fitar yace dakarunsu sun kuma kwato makamai daga hannun ‘yan bindigar da suka hada da bindigogi samfurin AK-49 da AK-47 da alburusai da babura da kuma wayoyin Saluda bayan kashe wasu 29 da kubutar da 52 daga cikin Wadanda aka yi garkuwa dasu
A cewarsa, Rundunarsu ta yi wa mayakan Boko Haram da na ISWAP kwanton-bauna akan hanyar Uzoro-Gadamayo da ke jihar Adamawa.
Kazalika sojojin tare da hadin-guiwar ‘yan sa-kai na Civilian Joint Task Force sun kama wasu mutane da ke yi wa ‘yan ta’addar safarar kayayyakin amfani, inda aka bayyana sunayensu da Hussain Dungus da Ali Bulama Jidda da Malam Ali Abuna.
Daga cikin kayayyakin da aka gano a hannun wadannan ‘yan safarar har da kudin da yawansa ya kai Naira miliyan 1 da dubu 797 da kuma 700, sai kuma nau’ukan abinci da wayoyin salula da babura da dai sauransu.
Har ila yau, sojojin na Najeriya sun yi luguden wuta kan ‘yan ta’addar a Karamar Hukumar Gwoza ta jihar Borno, inda suka ce, sun kashe wani kwamandan ISWAP mai suna, Alhaji Modu da aka fi sani da Bem Bem da kuma wasu mayakansa 20.