Masu yaki da rashawa a Najeriya na sukar wani yunkuri da aka ce tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye ke yi na sauya-sheka zuwa Jam`iyyar Labour da nufin neman takarar kujerar sanata ta mazabar Filato ta tsakiya.
Wasu dai na ganin cewa bai kamata mutumin da kotu ta kama da laifin badakala na makudan kudade ya sake neman shugabancin al`umma ba.
A ranar Litinin ne aka saki tsohon gwamnan da wasu daga gidan yari, bayan ya shafe kusan shekara hudu a daure, sakamakon kama shi da laifin wawure kudin gwamnatin jihar fiye da naira miliyan dubu daya.
Kasa da mako guda da sakin tsohon gwamnan, maganar sake tsayawa takararsa domin neman kujerar Sanata a mazabar Filato ta tsakiya ta fara fitowa kuma a hankali maganar sai kara karfi take yi.
Har a rahotanni ana cewa an kammala shirin karbar sa a jam`iyyar Labour tare da share masa hanyar shiga takara.
Sai dai masu yaki da rashawa a Najeriyar na cewa bai kamata a ba shi wannan damar ba, ganin cewa dawowarsa ke nan daga gidan yari, sakamakon daurin da aka yi masa, bayan kotu ta kama shi da laifin cinye kudin jihar ta Filato a zamanin da yake gwamna.
Auwal Musa Rafsanjani shi ne wakilin kungiyar Transparency International a Najeriya kuma ya bayyana cewa wannan ya nuna cewa yaƙi da cin hanci da rashawa da ake yi a Najeriya ya zama wasan yara.
“Idan Buhari ya ce ya yafe, ai jama’ar da aka sace kuɗinsu waɗanda suna nan suna fama cikin wahala da yunwa da talauci ai su ba su yafe ba,” in ji Rafsanjani.