Bankin Duniya zai kashe zambar kudi har Naira Biliyan daya da digo takwas wajan gyaran makarantun sakandire 614 da tallafawa dalibai a jihar Kano.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin jawabin mataimakin shugaban gudanar da aikin Alhaji Nasuru Abdullahi, a ziyar da yakai fadar maimartaba sarkin Bichi Alhaji Nasuru Ado Bayaro.
Abdullahi yace a cikin shirin mata 38,000 zasu Sami horo a Fannin sabuwar kimiyar zamani, kuma Kowacce makaranta an tsara mata aikin da zaayi mata da kudin da za a kashe mata.
Kazalika yace Akwai shirin wayar da kan dalibai wanda Shima za a gudanar dashi cikin wannan lokacin.