Tinubu ya nada kwamitin mata masu yakin neman zaben sa babu matar Osinbajo

Jam’iyya mai mulki a Nijeriya ta APC, ta sanar da nada Matar shugaban kasa Aisha Buhari a matsayin wadda zata jagoranci mata a kamfen din jami’iyyar na 2023, a yau asabar.

Kwamittin mai taken “Tawagar mata masu kamfen din Tinubu/shattema” ana sa ran uwargidan shugaban kasa itace zata zama shugabar wannan tawagar.

Sauran wadanda zasu taka rawa a tawagar sun hada da Sanata Oluremi Tinubu, Sanata mai wakiltan Legas ta tsakiya a zauren majalisar dattawa a wa’adi na uku a majalisar dattawa kuma tsohuwar uwargidan tsohon gwamnan jihar Legas, Nana Shettima, tsohuwar uwargidan gwamnan jihar Borno kuma uwargidan dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Tawagar  zasu yi aiki ne a matsayin Shugaba da Mataimakan Shugabanin tawagar kamfe a bangaren mata.

Wannan dai na kushe ne cikin wata sanarwa da Rinsola Abiola, diyar marigayi Cif MKO Abiola, kuma jigo a jam’iyyar APC ta fitar, wadda ita ma mambace a cikin kwamitin yada labarai na gudanarwar tawagar.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments