Binciken masana kan hanyar magance warin kashi.

Daga Walid Hari.

Warin kashi wata halittace da aka ajiyeta jikin dan adam mai rai, jiki yana fitar da sinadarin gumi sabida karancin isakar da yake samu ko yayin daya jigata ta hanyar wahala wannan yasa jiki kan fitar da wani ruwa mai wari ko wani yanayi mara dadi.

Wannan ake kira warin kashi, wanda mafi yawa yafi fitowa daga Hamata ko Mara sabida matattarar gashi ne. Masana sunce tsaftace wuraran biyu yanasa dan adam jin dadin jikinsa.

Mafi yawan lokuta masuyin warin kashi basaji sai dai wanda yake kusa dasu yaji musu, wanda hakan kansa mutum jin kunya musamman cikin samari da yammata.

Masana sun bayyana hanyar magance warin kashi ba lallai saida turareba domin amfani da turare kadai kan bada wani yanayi mara dadi.

Masanan sunce Sanya alumu a hamata ko mara yayin da akai wanka ko aka wanke wuraran yana kawar da kaso 90 cikin 100 na warin kashi.

Alumu baya cutar da fatar dan adam ko bata wata matsala wannan yasa ake amfani dashi.

A gwada wannan hanya.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments