An rahoto cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya yanke shawarar nada Lateef Fagbemi a matsayin atoni janar na tarayya kuma ministan shari’a
Fagbemi ya kasance babban lauyan da ke kare Tinubu da APC a kotun sauraron kararrakin zaben Shugaban kasa
Tinibu da jam’iyyarsa sun nada babban lauyan Najeriyan ne jim kadan bayan INEC ta sanar da Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023