FCT Abuja – Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Nosa Semota a matsayin mai ɗaukar hotonsa na kai da kai awanni bayan shiga Ofis a karon farko.
A ɗaya bangaren an naɗa Ope Adelani a matsayin mai ɗaukar hoton ofishin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, yayin da suka fara zangon mulki na tsawon shekara huɗu.