Ana cigaba caccaki shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa naɗin da ya yi kwanan nan na Taiwo Oyedele, wani masani kan haraji a PwC sannan na gaba-gaba wajen caccakar gwamnatinsa.
Phrank Shuaibu, hadimin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, a cikin wata sanarwa da Legit.ng ta samu a ranar Asabar, 8 ga watan Yuli, ya ce akwai wata a ƙasa kan naɗin da Tinubu ya yi wa mai caccak
Ya bayyana cewa yawan ganawar da Tinubu yake yi da ƴan adawa wani salo ne na kulle bakunansu.
A kalamansa: yace
“A bayyane yake cewa Mr Oyedele yana daga cikin masu caccaka kan sake fasalin haraji. Ranar Asabar ɗin da ta gabata ya nuna wasu kura-kurai kan shirye-shiryen haraji na gwamnatin APC.”
Domin a kulle bakinsa, sai aka naɗa shi shugaban kwamitin sake fasalin haraji a ranar Juma’a, amma ba a sanar da sauran mambobin ba, ƙila suna son ya yi aiki shi kaɗai ne.”
An buƙaci Oyedele da kada ya bari Tinubu ya janye masa hankali
Shuaibu ya yi nuni da cewa naɗin da aka yi wa Oyedele ba zai ba shi damar sake yin magana kan wani abu wanda ba daidai ba ne dangane da gwamnatin.