Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari ya na hannun jami’an hukumar DSS
Jaridar Punch ta ce zuwa yanzu babu wanda ya san dalilin tsare Abdulaziz Yari sanata mai wakiltar Zamfara ta yamma a majalisar dattawan kasar nan.
Wata majiya ta ce Yari ya kai kan shi ne zuwa ofishin hukumar DSS bayan zaman majalisar tarayya da aka yi a ranar Alhamis da ta wuce.
Hakan na zuwa ne bayan jami’an tsaron sun aikawa fitaccen ‘dan siyasar goron gayyata kamar yadda wani na kusa da shi ya shaida.
“Sanata Abdulaziz Yari ya na hannun DSS, amma da yardar Ubangiji ba zai dade ba zai fito. Ya je ofishinsu ne bayan zaman majalisa.
A wani rahoto da ya fito daga Peoples Gazette, ana zargin cewa DSS ta cafke Sanata Yari ne saboda ya ki amsa wayar shugaban hukumar.
Rahoton jaridar The Nation ya nuna jami’an DSS sun bukaci ganin Yari ne saboda yana neman kawowa Godswill Akpabio cikas a majalisar dattawa.
A gefe guda kuma jaridar Sahara Reporters ta ce Yari ya samu kan shi a matsala ne bisa zargin Gwamnan CBN ya ba shi N45bn domin yakin neman zabe a 2019.