Gwamnatin Kano ta ja kunnen yan jaridun dake aiki a fadar Gwamnatin jihar

Daga  ADAMU DABO

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Baba Halilu Dantiye yayi kira ga ‘yan jaridun dake aiki a fadar gwamnatin jahar Kano da su zama masu gaskiya,adalci da bayyana sahihan labaran gaskiya domin Alummar jihar Kano

Baba Halilu yayi Kiran ne yayin wata ziyara ta musamman da ayarin ‘yan jaridun dake fadar gwamnatin jihar Kano suka Kai masa a ma’aikatar yada labarai

Dantiye ya ja hankalin ‘yanjaridun da su zama masu gaskiya, adalci da yada labarun gaskiya domin Gwamnatin Mai girma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a shirye take domin Samar da shiye -shiye managarta domin cigaban Alummar jihar Kano

Tun da fari a nasa jawabin shugaban ‘yanjaridun da ke fadar gwamnatin jihar Kano Adamu Dabo ya ce sun kawo ziyarar ce domin taya kwamishinan murnar samun wannan matsayi da Kuma samun kyakkyawar alakar aiki da shi

Adamu Dabo ya Kuma ja hankalin ‘yanjaridun fadar gwamnatin jihar Kano da su zama masu aiki tukuru wajen Samar da labaran gaskiya ga Alummar jihar Kano

Covered/govt House/Dabo

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments