Tinibu ya mika sunayen ministoti ga hukumar EFCC da DSS dan tantance su

 Shugaba Bola Ahmed Tinubu bayan ya shafe kwanaki 40 a ofis, jama’a na sauraron wadanda za a zaba su zama Ministoci.

A Rahoton jaridar  Punch na ranar Litinin, an samu labari ‘yan majalisa sun fara damuwa kan abin da ya hana aiko sunayen wadanda za a baiwa mukamin  Ministoti

Wasu Sanatoci da su ka yi magana ba tare da bari an kama sunayensu ba, sun ce ba su tunanin za a cigaba da bata lokaci kafin a fitar da Ministocin.

Majiya mai tushe ta shaidawa jaridar cewa jami’an EFCC da DSS da sauran hukumomin tsaro su na daf da kammala binciken wadanda ake sa ran su zasu rike mukamin ministocin

Hukumar DSS ta fararen kaya da na hannun-daman shugaban kasan su na tantance wadanda aka zaba kafin a fitar da sunayensu zuwa ga majalisar dokoki.

Tsohon ‘dan majalisar tarayya, Hon. Alex Egbona ya ce dole ne a sanar da Ministoci cikin watanni biyu, ya na sa ran ba zai wuce makon yau zuwa gobe be.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments