Kamar yadda aka saba, bayan zaɓen duk wani shugaba a kowanne mataki, shugaban na tashi ya yi godiya ya kuma bayyana irin alƙawuran da zai cika a yayin jagorancinsa.
Irin haka ce ta faru ga shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu bayan zaɓar da aka yi masa a matsayin sabon shugaban ƙungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, Ecowas.
Kakakin Shugaban Najeriya Abdul’aziz Abdul’aziz ya yi wa BBC ƙarin bayani game da zaɓen Tinubu da kuma bayanan da ya gabatar bayan zaɓen nasa.
“Ƙimar Najeriya na ƙara bunƙasa a idanun ƙasashen Afrika da Duniya baki ɗaya, kuma wannan dalili ya sa suka bai wa Shugana Bola Ahmed Tinubu jagorancin wannan ƙungiya.
“Ka tuna bai yi wata biyu ba cikakku kan mulki amma darajar ƙasar da kuma shi kansa ta sa suka ba shi jagorancin,” in ji Abdul’aziz.
Tinubu ya zayyana abubuwa uku da zai bai wa muhimmanci waɗanda suka haɗa da:
Tsaro da zaman lafiya
Duk da cewa abu ne sananne cewa yankin ƙasashen da suka haɗa ƙungiyar na fama da matsalar tsaro amma Tinubu ya jadada buƙatar kawo ƙarshen matsalar saboda muhimmancin da take da shi.
“Game da zaman lafiya da tsaro, barazanar takai matakin ƙololuwa da ya zama wajibi a ɗauki matakan gaggawa domin shawo kan ƙalubalen,” in ji sabon shugaban.
“Babu shakka ƙarancin zaman lafiya a yankunanmu zai ci gaba da daƙile ci gabanmu, kuma yankin mu ya ci gaba da zama a baya.
A wannan gaɓa, dole mu nuna damuwa da ci gaba da amfani da tsare-tsaren da muka kawo domin ganin ƙarshen matsalar tsaro,”
Matsalolin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai irinsu, Boko Haram da ISWAP ko shakka babu na haifar da koma baya a ci gaban yankin, ECOWAS in ji Tinubu.