Babbar kotun tarayya dake zamanta a birnin tarayya Abuja ta umurci gwamnatocin da suka yi ikirarin sun karbo kudaden da ake zargi tsohon shugaban kasa marigayi Janar Sani Abacha ya boye a kasashen ketare.
Kotun da mai sharia James Kolawole Omotosho, yake jagoranta ta umarci gwamnatocin ne da suka hadar da gwamnatin Obasanjo da ta Umaru Musa yar’aadu, da ta Goodluck Ebele Jonathan, da gwamnatin baya-bayan nan ta Muhammadu Buhari.
A cewar kotun wadannan gwamnatoci sun karbo zunzurutun kudi har dalar Amurka Biliyan biyar inda ta umarci ma’aikatar kudi da ta mika rahoton yadda aka kashe kudaden ga hukumar SERAP.