Hukumar Tarayyar Turai (EU) ta yanke shawarar nada Marion Lalisse a matsayin mai kula da harkokin yaki da kyamar Musulunci, mukamin da ya shafe watanni 18 ba tare da kowa ba.
A wata sanarwa da ta fitar ta shafinta na Twitter, Lalisse ta ce tana alfahari da nadin nata.
Ta ce, “Al’amari ne mai muhimmanci da ke bukatar hadin gwiwa da himma.”
A cikin wata rubutacciyar sanarwa da Hukumar EU ta fitar dangane da nadin, an bayyana cewa Lalisse za ta yi aiki tare da kasashe mambobin EU, cibiyoyi na Turai, kungiyoyin fararen hula da jami’o’i, kuma za ta kasance wacce kungiyoyin da ke aiki a wannan fanni a cikin EU za su tuntuba.
Mambar Hukumar EU da ke da alhakin samar da daidaito, Helena Dalli, wadda bayananta ke kunshe a cikin sanarwar, ta yi nuni da cewa ya kamata a yaki kyamar Musulunci a dukkanin bangarori na rayuwa, da suka hada da ilimi, aikin yi da kuma zamantakewa, sannan a tattara bayanai kan dukkan al’amura a cikin wannan lamari.
Marion Lalisse, wacce a baya ta yi aiki a ofisoshin diflomasiyya na EU a Yemen, Morokko, Ghana, Mauritania da Jamhuriyar Turkawan Arewacin Cyprus, ta iya Larabci.
An soki EU da barin wannan mukamin ba tare da kowa ba a lokacin da kyamar Musulunci ke karuwa a Turai.