Yaduwar zazzabin Lassa, NCDC na shirin kakaba dokar ta baci

A kokarin ta na yakar cutar lassa yanzu haka hukumar NCDC na shirin  kakaba dokar ta baci a fadin kasar nan inda tace zazzabin na cigaba da yaduwa daga dabbobi zuwa mutane kuma yana iya yin kisa.

Daraktan Cibiyar hukumar Yaki da Cututtuka masu yaduwa  ta kasa wato  (NCDC), Dakta Ifedayo Adetifa shine  ya bayyana cewa saboda karuwar masu kamuwa da cutar, an kafa dokar ta baci tare da fara gudanar da bincike kan cutar.

A watan Janairu mutane 37 ne suka mutu a kasar sakamakon cutar, wacce aka gano a cikin mutane 244.

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa an gano wasu magunguna guda 3 da za su yi maganin cutar.

A annobar zazzabin Lassa da ke tsanani a tsakanin watan Nuwamba zuwa Mayu, lokacin zafi a duk shekara, mutane 178 ne suka mutu a shekarar da ta gabata, inda aka gano mutane 989 da suka kamu da cutar.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments