APC ta bayyana kuskuren Abdullahi Adamu na kin rungumar sulhu

Lanre Isa-Onilu ya tofa albarkacin bakinsa a kan abubuwan da su ke faruwa a APC da har ya kai ga shugaban jam’iyya ya ajiye matsayinsa.

Lanre Isa-Onilu wanda ya taba zama Sakataren yada labarai a jam’iyyar APC, ya zanta da Vanguard kan rikicin cikin gidan da ya barko masu

A ra’ayin tsohon kakakin jam’iyar mai-mulki, babban kuskuren Sanata Abdullahi Adamu bayan ya karbi shugabanci shi ne watsi da shirin sulhu.

Isa-Onilu yake cewa Adamu yana maye gurbin Mai Mala Buni a majalisar NWC, sai ya ajiye batun sasancin da ake ta kokarin yi tun kafin ya shiga ofis.

Bayan maganar yi wa ‘yan jam’iyya da ke rikici sulhu, ‘dan siyasar ya ce Adamu ya yi kuskure wajen goyon bayan wani ‘dan takara a zaben fidda gwani.

“A matsayin shugaban APC, za ayi tsamannin ba zai nuna bambanci a jam’iyya ba. Ya kamata ya zama bai dauki bangare ba, amma bai yi ba.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments