Sojojin kasar Turkiyya sun ci gaba da tsare kambun su a Duniya

Rundunar Sojin Türkiye (TSK) ta ci gaba da zama a matsayin ta na 11 a fannin fasahar aiki cikin jerin kasashe 145 kamar yadda ta kasance a shekarar 2022.

Shafin yanar gizo na Global Firepower na kasar Amurka, wanda ke nazari kan karfin soji na kasa da kasa, shine ya fitar da jerin sunaye na shekarar 2023.

Sanarwar mai dauke da jerin sojojin kasashe 145 tace ta fitar da jadalin ne ta hanyar yin la’akari da abubuwa kamar ci gaban fasaha, karfin aiki da kuma dadewa a fagen daga.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments